Wani majiya ya shaida mana cewa ganawar da jiga-jigan suka yi zata kulla kyakkyawar alaka tsakanin tsofafin abokan hammaya kuma ana kyautata zato cewa Obasanjo zai bude kofar sa na mara ma Atiku baya a zaben 2019 domin kayar da anniyar shugaba Buhari na zarcewa a saman kujerar mulkin Nijeriya.

Martanin fadar shugaban kasa

A cikin sanarwa da hadimin Shugaba Buhari kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce ba su yi mamakin labarin da ke cewa Obasanjo yana goyon bayan Atiku a zaben 2019 dmin dukansu ba za su yi nasara ba.

"Ba mu manta ba kuma 'yan Najeriya su ma suna sane cewa kimanin shekara 11 da ta wuce ne tsohon shugaban da kuma tsohon mataimakinsa a kokarinsu na neman mulki suka zargi juna da aikata cin hanci da karbar rashawa," in ji Malam Garba Shehu.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana , Atiku ya isa zauren gidan Obasanjo a daidai karfe 1:05 na rana tare da wasu jiga-jigan PDP da wasu manyan malaman addini.

Cikin tawagar da suka garzaya gidan tsohon shugaban kasa akwai shugaban jam'iyar PDP, Uche Secondus, jagoran kungiyar Afenifere, cif Ayo Adebanjo, shugaban yakin neman zaben Atiku, Gbenga Daniel da Sanata Ben Murray-Bruce.

A bangaren malamai kuwa akwai Bishop Mathew Kukah, Bishop David Oyedepo da kuma Sheikh Ahmad Gummi.