ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Yadda yan majalisa suka tarbi Sanata Ndume bayan dakatarwar da aka yi masa na tsawon wata 7 (Hotuna)

Ndume ya shigo farfajiyar majalisar dattawa kamar yadda ya saba cikin fararen kaya

Dan majalisar dattawa mai wakiltar jihar Borno Ali Ndume ya dawo farfajiyar majalisa ranar laraba bayan wata 7 da samun dakatarwa daga majalisar.

A cikin watan Maris na bana aka dakatar dashi bisa ga wani rahoto da kwamitin ladabtarwa ta musaman ta bayyana ma majalisar inda aka kama dan majalisar da yi ma shugaban majalisar Bukola Saraki da sanata Dino Melaye kake.

Yayin dawo majalisar sauran abokanan aikin sa sun tarbe shi da hannu bibbiyu inda shima ya zaisa da su cikin farin ciki da walwala.

Bayan zaman sa a kujerar sa shi dai wannan da majalisar ya bukaci sauran yan majalisar da su bashi damar kara yin jaje game da rasuwar marigayi sanata Isiaka Adeleke wanda ya rasu yayin da yake cikin dakatarwa.

ADVERTISEMENT

Bayan zaman su a zauren su, Ndume ya shaida wa manema labari cewa ya kai kara kotu domin samun amsar tamabaya na, abun da majalisar tayi masa daidai ne ko ba daidai bane? kuma kotu tace ba daidai bane amma duk da haka majalisar tace zata daukaka karar.

Shi dai dan majalisar ya sanar ma mane labarai cewa daga nan kasar Saudiya zai tafi domin kaddamar da aikin Umra don nuna godiya.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT