Pulse.ng logo
Go

Gasar karrama yan wasan arewa Fitattun jarumai da suka yi nasarar lashe kyaututuka a gasar AMMA

Ado Ahmad GIdan Dabino, Bello Hafizu Halima Atete da Ali Nuhu na daga cikin fitattun jarumai da tauraron su ya haska a gasar bana

  • Published: , Refreshed:
Ado Ahmad Gidan Dabino play

Ado Ahmad Gidan Dabino

(Instagram/gidandabino)

A karshgen hutun makon da ya gabata, jarumai da masu ruwa da tsaki har da mawaka da masu bibiyan fina-finai hausa sun garzaya zuwa jihar domin halartar gasar karrama fitattu.

Gasar Arewa Music and Movies Award (AMMA), gasa ce wanda ake shiryawa a ko wani shekarar domin karrama fitattun jaruman da mawakan Arewa da suka taka rawar gani a sana'ar su.

Jaruma ta amshi kyautar gwarzuwar shekara play

Jaruma ta amshi kyautar gwarzuwar shekara

(Instagram/haleemaatete)

 

Bikin taron wanda aka gudanar a jihar Katsina a karshen makon da ya shude, ya samu halarcin fuskoki da dama na daga jiga-jigan masana'antar kannywood.

Wasu daga cikin manyan jarumai da suka yi nasara lashe kyaututuka a gasar sun hada da;

Bello Hafizu - ya amshi lambar yabo guda biyu

Bello Hafizu tare da Hamisu Iyantama play

Bello Hafizu tare da Hamisu Iyantama

(Instagram/bellohafizu)

 

Isa A. Isa - Shima ya samu lambar yabo guda biyu

Isa A. Isa play

Isa A. Isa

(Instagram/isaaisa)

 

Ado Ahmad Gidandabino - Shine jarumin jarumai a gasar bana, tauraron shi ya haska matuka bisa kwarewa da nuna basira da aka yi a shirin "Juyin sarauta". Ya samu kyauta har guda shidda a dare daya.

Ado Ahmad Gidan Dabino play

Ado Ahmad Gidan Dabino

(Instagram/gidandabino)

 

Halima Atete - ta samu kyuatar  zama gwarzuwar shekara

Ali Nuhu - an bashi kyautar fitaccen mai bada umarni na bana bisa rawar da ya taka wajen shirya fim din 'Mansoor".

Umar M.Sheriff da Ali Nuhu sun amshi kyuat bisa rawar da suka taka a shirin "Mansoor" play

Umar M.Sheriff da Ali Nuhu sun amshi kyuat bisa rawar da suka taka a shirin "Mansoor"

(Instagram/realalinuhu)

 

Sauran jarumai da suka samu kyauta a daren sun hada da Ali Jita, Umar M. Sheriff, Amal Umar, Hafsat Idris da sauran su.

Taron bikin gasar na bana ya tada kura ya bar baya ganin yadda dandazon jarumai da ma'abotan fina-finai da wakokin hausa suka bayyana a garin Katsina domin taya juna murna.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.