Pulse.ng logo
Go

Aikin hajjin bana Mansura Isa da Saratu Daso a kasa mai tsarki

Jaruman sun tashi tare da mahajjatan jihar Kebbi kuma matar gwamnan jihar ta dauki nauyin aikin su.

  • Published:

Tsohuwar jarumar fim kuma uawargidan fitaccen jarumi, Mansura Isa tare da tauraruwa Saratu Gidado Daso sun ketara kasa mai tsarki don yin aikin hajji na wannan shekara.

Kamar yadda suka sanar matar gwamnan jihar Kebbi Hajiya Zainab Atiku Bagudu ta dauki nauyin tafiyar su.

 

Jaruman sun gaza boye farin cikin su na kasancewa cikin wadanda Allah ya nufa zasu gudanar da aikin hajji na wannan shekarar.

A shafin ta na kafar sada zumunta, Mansura Isa ta rubuta "Allah ya saka miki da alheri mummy".

View this post on Instagram

#pilgrimage MADINA

A post shared by Saratu Gidado Daso (@saratudaso) on

 

Sun wallafa hotunan su yayimn da suka dirar kasar Saudiya tare da yi ma uwargidan gwamnan godiya bisa halaccin da tayi masu.

Tun a makon da ya shude maniyata daga Nijeriya suka fara tafiya kasar Saudi Arabia don gudanar da aikin hajji na wannan shekara.

Kamar yadda hukumar hajji na kasa ta sanar, kai ga yanzu akalla mahajjata 14,160 aka garzaya dasu kasar.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement