ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Majalisar Kano ta amince da sabon mataimakin gwamna Ganduje

Majalisar ta tabbatar da haka zaman da tayi ranar Talata 18 ga watan Satumba karkashin jagorancin kakakin majalisar, Kabiru Rurum.

Nasiru Gawuna

Dan majalisa Zubairu Masu mai wakiltar karamar hukumar Sumaila a majalisar ya shigar kuddurin amince da Gawuna bayan da gwamnan ya tura sunansa majalisar don neman amincewar su.

Dan majalisar yayi la'akari da matsayin da Gawuna ya rike na zama kwamishnan noma a wa'adi biyu wajen shawo kan sauran yan majalisar domin tabbatar dashi.

Sabon mataimakin zai maye gurbin tsohon mataimakin gwamnan jihar farfesa Hafiz Abubakar wanda ya sauka daga mukamin sa cikin watan Agusta.

ADVERTISEMENT

Tsohon mataimakin gwamnan ya dauki matakin ajiye mukamin sa a gwamnatin jihar bisa wasu dalilai na rashin jituwa tsakanin sa da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje.

Gabanin wannan mukamin, tsohon kwamishnan ya taba zama shugaban karamar hukuma kana ya rike mukamin shugaban hukumar wasanni ta matasa na tarayya.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT