ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Majalisar dattawa ta taka wa gwamnatin Kaduna birki, ta hana ta ciyo bashin $350M

Wannan watsin da akayi da batun bashin ya biyo bayan rahoton kwamitin kula da basusuka na majalisar wanda shugaban kwamitin Sanata Shehu Sani ya mika a gaban ta

Wannan watsin da akayi da batun bashin ya biyo bayan rahoton kwamitin kula da basusuka na majalisar wanda shugaban kwamitin Sanata Shehu Sani ya mika a gaban ta.

Kamar yadda masu sharhi suka bayyana, yunkurin hana karban wannan bashi da shugaban kwamitin majalisar ya mika na da nasaba da rikicin da ke tsakanin shi sanata Shehu Sani da gwamnan jihar Malam Nasir El-Rufai.

Daya daga cikin dalilan da ya sa Shehu Sani ya ce ba zai goyi bayan gwamnatin jihar Kaduna ta sami wannan kudin ba shine, ganin cewa jihar Kaduna ce na biyu a jerin jihohin kasar da bashi yayi wa katutu.

Yace jihar Kaduna na da wadatar kudaden da take bukata domin gudanar da ayyukan ta ba tare da ta ciyo irin wannan dimbin bashi ba.

ADVERTISEMENT

Sanatoci uku da ke wakiltar Kaduna  a zauren majalisar dattawa duk sun ki amincewa da wannan bashi. Da suke tofa albarkacin bakin su a zauran majalisar lokacin da ake muhawara a kan batun, dukkanin su sun ce ba za su goyi bayan jihar ta sami wannan bashi ba.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT