Wani direba ya gamu da izar jamian tsaro inda wani soja ya umarce shi da ya sauka daga motar sa don yin tsallen kwado.

Direban ya game da wannan hukuncin bisa laifin tare hanyar babur din da sojan ya hau.

A cikin bidiyon da aka fitar a dandalin sadarwa an gan inda direban ke bin umarnin da aka bashi na yin tsallen.

Lamarin ya faru a hanyar dake kusa da barikin sojoji na Signal Baracks dake nan unguwar Mile 2 dake jihar Legas.