ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Babu jinkiri wajen kama masu aikata laifi

Shugaban hukumar yaki da rashawa yace hukumar zata hada gwiwa da sauran hukumomin na kasashen waje don gano kudade da barayin gwamnati suka sata

Mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa na kasa (EFCC) ya bayyana cewa hukumar bata jinkiri wajen kama masu satar kudin jama’a don jinkiri yana da hadari.

Ibrahim Magu ya bayyana haka ne a jihar Legas yayin da ya ziyarci gidan jaridar Punch ranar alhamis 7 ga watan Satumba.

Dangane ga nasarori da cimma burin hukumar shugaban yace hukumar zata hada gwiwa da sauran hukumomi dake kasashen wajen wajen gano kudade da barayin gwamnati suka sata.

Magu yace ya zama dole a yaki cin hanci da rashawa  a wannan zamani don al’umma na gaba su samu rayuwa mafi inganci.

ADVERTISEMENT

A karshe shugaban yayi kira ga ‘yan kasa da su hada gwiwa da hukumar don taimakawa wajen kawar da wannan mummunar laifi kafin ya mamaye mu don kuwa shine babban matsala a kasar

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT