ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

An fitar da littafi kan rayuwar shahararren mawaki Dr Mamman Shata

Marubucin yace ya shafe shekarar 12 yana aikin fitar da littafin kuma wannan ya sha bambam da wanda aka rubuta cikin shekara 2006.

Shahararren dan jarida kuma marubuci Ibrahim Sheme ya rubuta littafin mai dauke da shafuka 921.

Tsawon shekara 12 yayi yana aikin fitar da littafin na tarihin rayuwar fitaccen mawakin.

Marubucin yace bai taba rubuta littafi wanda ya sha wuya kamar wannan.

ADVERTISEMENT

Yana mai cewa "Na kashe kudi ban san adadin su ba. Na rika zama a tebur, a gaban komfuta, daga safe zuwa karfe 2 na dare, na tsawon watanni, na hana kai na more rayuwa yadda ya kamata, kafin wannan aiki ya kammala".

Ibrahim Sheme yace wannan littafin wanda Shata da kanshi ya bashi izinin rubutawa ya sha babban da wanda yayi jagoran rubutawa a shekarar 2006.

Yace littafin ya inganta ta fuskoki daban-daban kuma ko makaho ya zai ji bambamcin ta idan ya shafa.

Masana sun gudanar da taron nazari kan rayuwa da fasahar shahararren mawakin ranar litinin 3 ga watan Satumba a nan sashen hausa na jami'ar Bayero dake Kano.

Dr Mamman Shata yayi fice a gida da wajen Nijeriya zamanin baya. Ya rasu a cikin shekarar 1999 a nan asibitin Aminu Kano bayan wata rashin lafiya da yayi.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT