Pulse.ng logo
Go

Layya mai tsada Wani mutum ya samu belin N40,000 don ya saci rago mai kimanin N40,000

Bisa ga labarin dan sandan da ya gurfanar dashi sifeto Samad Aliyu, Saka ya saci ragon tare da taimakon abokanan sa

  • Published:
Wani ya samu ragon layya da tsada play

Wani ya samu ragon layya da tsada

An gabatar da Wani Kasimu Saka mai shekara 41 a gaban kotu hukunci dake Ibadan ranar laraba bisa ga zargin satar rago mai kimani naira N40,000.

Dan sanda wanda ya gurfanar dashi sifeto Samad Aliu ya fada ma kotu cewa Saka tare da abokanan sa sun hada baki suka saci ragon mallakar wani Mista Adesola Adeyemi dake zama a unguwar Fagbemi dake ring road nan garin Ibadan.

Ya fada ma kotu cewa sun aikata laifin a daidai karfe 8:00 na daren ranar 21 na watan agusta a nan unguwar Fagbemi.

Laifin da ake zargin shi da aikatawa ya sanawa kundin tsarin jihar Oyo na 2000 a dai dai sashen 390 da 516.

Mai laifin ya nemi kotu da ta sassauta hukunci.

Mai sharia Mrs Patricia Adetuyibi ta zartar da hukunci mai cewa kotu ta bashi damar yin beli a kan N40,000 yayin da ta daga ranar sauraron karar zuwa 4 ga watan octoba.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement