ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Kaico! An samu takaddamar cutar amai da gudawa a jihar kwara

Comisional lafiya na jihar Dr  Atolagbe Alege ya tabbatar ma yan jarida cewa an samu fitowar annobar a wasu anguwanni a garin ilorin babbar birnin jihar.

Kaico! An samu takaddamar cutar amai da gudawa a jihar kwara

A wani ganawa da yayi da yan rehoto na  News agency of Nigeria (NAN), Dr Alege yana ikirari cewa ita wannan cutar bata kai ga rashin rai ba.

Yace mutanen da suka kamu da wannan cutar sun kunshi manya hudu(4) da yara biyu(2).

Ya kara da cewa unguwanni da wannan annobar ta faru sune, Ogidi, Oko-Olowo, Pakata, Oloje da Alore duk a hukumar birnin Ilorin.

ADVERTISEMENT

Alege ya fada cewa an sallamo mutum hudu cikin shida daga asibiti sauran mutane biyu suna gab da sallama daga asibiti dan ana basu kulawar daya dace a asibiti.

Ya kara da cewa abun da ya haifar da wannan cutar shine rashin kulawa da wanke  ya’yan itatuwa yayin bude baki a wannan lokacin azumi wato ramadan.

Yace Gwamna Abdulfatah Ahmed ya umurci hukumar da su samo ma unguwannin tsaftacciyar ruwa da gaggawa.

"Babban ministan Lafiya ya tsananta da yin kamfe na masaniya don jawo hankalin mutane kan cutar amai da gudawa da ire-iren sa.

"Asibitoci hudu na gwamnati aka ƙaddamar da su dinga kulawa da wannan annobar, babban asibitin jiha zata kasance gurin riko.’’

ADVERTISEMENT

Ya umurci mutanen garin dasu yaba ma gwamnatin jihar a kan fito na fito da takeyi an kan samar ma mutane lafiyayen gari a ko wani lokaci.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT