Pulse.ng logo
Go

Labarin ƙwallo Mai tsaran gidan Arsenal ya koma West brom da wasa

est brom ta sanar cewa ta siya dan wasan daga Arsenal a yarjejeniyar da zai zashi ya zauna a ƙungiyar har shekara 4

  • Published:
Gibbs ya koma West brom play

Gibbs ya koma West brom

Dan wasan ƙasar England Kieran Gibbs ya koma West brom da wasa, ƙungiyar ta sanar da haka ranar laraba.

West brom bata bayyanar da kudin da ta siya dan wasan mai shekara 27 amma kafafan watsa labarai na ƙasar Ingila suna yada labari cewa wata kila a kan pam miliyan bakwai (£7M) ƙungiyar ta siye shi.

Gibbs dai ya fara wasa ma Arsenal tun yana matashi ya buga wasanni da dama ma ƙungiyar.

Dan wasan ya saki sako a shafin sa na twitter inda yake ma ma’aikatan Arsenal da masoyan ƙungiyar godiya kuma ya kara da cewa buga ma  Arsenal tamkar kamar mafarki ne wanda ya zama zahiri a wajen shi.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.