Pulse.ng logo
Go

Labarin kwallo Yan Africa 6 da ake sa ran cewa zasu yi balaguro zuwa sabon kulob

Ga wasu yan wasan nahiyar africa da muke ganin cewa zasu bar inda suke yayin da ake rububin cinikayya kafin a rufe kasuwar saye da sayarwa na bana

  • Published:
Ahmed musa play

Ahmed musa

Yau kayyadajjen rana na cinikin yan ƙwallo nahiyar turai kuma ƙungiyoyi da dama na rububin siyan yan wasa kafin a rufe kasuwar.

Ga wasu yan afrika da muke tunanin zasu yi balaguro zuwa wani kulob da taka leda a wannan takaitacen lokacin cinikayya

1. Ahmed musa

wata kila zai koma ga tsohon cociyar shi play

wata kila zai koma ga tsohon cociyar shi

 

Dan wasan ƙasar Nigeria ya koma Leicester a kakar bara kuma yana shirin barin zakarun premier na 2016.

Kociyar ƙungiyar ya nuna alamu cewa baya bukatar dan ƙwallon tun da ya hau kujerar horarwa.

Hakika babu wuri da dan ƙasar Nigeria zai buga a Leicester tunda akwai sabobin yan wasa da ƙungiyar ta siya.

Tunda babu wuri wata kila dan ƙwallon zai koma ga tsohon kociyan shi sanda yake CSKA Moscow wanda ya sauya zuwa Hull city.

2. Riyad Mahrez

Riyad Mahrez play

Riyad Mahrez

 

Abu  mamaki ne ganin cewa har yanzu Mahrez bai tafi wani kulob ba bayan ya sanar ma Leicester cewa ya shirya barin ƙungiyar idan ya samu inda zai tafi.

Dan wasan tawagar ƙasar Algeria ya samu tayi daga kulob da dama. Yana da zabin zuwa Chelsea, Arsenal, Roma ko Barcelona tunda suna yakin ganin shi a tawagar su.

3.  Adama Traore

Adama Traore play

Adama Traore

 

Dan wasan ƙasar Mali yana cikin yan wasan da muke tunani zasu sauya zuwa sabon kulob.

Fittacen dan ƙwallon yana shirin barin Middlesbrough amma kulob din ba zai sake shi da arha ba duk da cewa kociyar Marseile ya nuna yana sha’awar dan wasan.

4. Diafra Sakho

Sakho play

Sakho

 

Da alamu kwannan Sakho ya kare a West ham tunda yana shirin barin ƙungiyar zuwa Ligue 1.

Stade Rennais na gaba gaba wajen ganin dan wasan a filin su.

5. Vincent Aboubakar

Vincent Aboubakar play

Vincent Aboubakar

 

Da alamu Aboubakar ya shirya kayan shi tunda Marseille dage wajen ganin dan wasan ya dawo France.

Karo na uku kenan da Marseille ke neman dan wasan tawagar Cameroon shin ko zasu ci nasarar samun dan wasan tunda Wolves suma sun nuna sha’awa?

6. Daniel Amartey

Daniel Amartey play

Daniel Amartey

 

 

A tsakiyar kakar 2015/2016 Amartey ya dawo Leicester inda shima ya taimaka wajen kafa tarihi lokacin da suka ci nasarar zama zakarun Ingila a wannan kakar.

Ganin cewa akwai ire-iren Wilfred Ndidi, Daniel Drinkwater, Vincent Iborra, Matty James, Nampalys mendy da Andy King wadanda aka tunanin suna gaba dashi a kulob din dole dan wasan Ghana ya shirya komawa wata kulob.

Stuttgart na Germany sun nuna sha’awar kawo dan wasan a filin su.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.