Anyi wata biki a garin Abuja ranar asabar bayan daura auren su ranar juma'a 16 ga watan maris a fadar sarkin Kano kuma ya samu halartar shugaban kasa da manya-manya yan siyasa da yan kasuwa.
Shagalin bikin auren Fatima Dangote da Jamil Abubakar a garin Abuja
Fitattun mawaka Iceprince zamani da Morell sun nishadantar da baki a taron bikin wanda aka gudanar a International conference center dake garin Abuja
Bikin auren nasu ya fara ne tun kafin ranar daurin aure inda aka yi shagulgula a jihar Kaduna da kano.
Washe garin ranar daurin auren su aka gudanar da wata biki a garin Abuja wanda ya samu halarta iyaye da yan uwa da abokan arziki.
Fitattun mawaka Iceprince zamani da Morell sun nishadantar da baki a taron bikin wanda aka gudanar a International conference center dake garin Abuja.
har ila yau dai shagalin bikin bai tsaya a nan ba domin za'a kara gudanar da wata a dakin taro na Eko Hotel dake jihar Legas a karshen mako.
JOIN OUR PULSE COMMUNITY!
Eyewitness? Submit your stories now via social or:
Email: eyewitness@pulse.ng