Al'ummar garin Azare sun fito a dandazon su domin tarban shugaban kasa
Shugaban ya kai ziyara jihar Bauchi domin jajanta ma gwamnatin jihar da al'ummar ta bisa ga guguwar iska da gobara da ta tashi kwanan baya.
Shugaban ya kai ziyara jihar Bauchi garin domin jajanta ma gwamnatin jihar da al'umar jihar masu bisa ga gobarar da ta tashi a kasuwar Azare da guguwar da ya faru.
Shugaban ya isa jihar safiyar ranar Alhamis 21 ga watan Yuni inda ya samu tarba daga gwamna Abubakar Muhammad da shugaban majalisar jihar tare da sauran jami'an gwamnati.
A ranar asabar da ya gabata aka yi mummunar guguwa a jihar wacce ta jawo duhu a garuruwa da dama.
Sakamakon ftila'i iskar mutane da dama sun mutu yayin da wasu kuma suka jikkata. An kuma samu asarar dukiyoyi.
Washen garin ranar Lahadi kuma an kuma samu tashin mummunar gobarar wuta a babbar kasuwar garin Azare duk a jihar wanda yayi sanadiyar asarar dinbim dukiya.
Kamar yadda rahotanni suka bayyana, gobarar ta cigaba da ci tun daga daren ranar Lahadi har safiyar ranar Litinin.
JOIN OUR PULSE COMMUNITY!
Eyewitness? Submit your stories now via social or:
Email: eyewitness@pulse.ng