A makon da ya gabata cikin Najeriya an samu fitowar muhimman labarai kama daga dandalin siyasa, nishadi da sauran su.

Ga kannun labarai da suka fito kamar haka;

Kwankwaso yayi barazanar ficewa daga jamiyar PDP

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma dan majalisar dattawa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, yayi barazanar ficewa daga jam'iyar PDP muddin uwar jam'iyar na Abuja ta cire yan akidar sa na Kwankwasiya daga cikin yan takarar ta a jihar Kano.

Kwakwaso dai yayi wannan barazanar ne a garin Abuja yayin da ya gana da wasu jiga-jigan jam'iyar PDP kan batun yan takarar jam'iyar daga jihar Kano.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana kwamitin ayyuka na PDP ta shirya taron ne domin sasanta ya'yan jam'iyar na jihar domin cinma matsaya da zai haifar da farin ciki a cikin zukatan ya'yan jam'iyar na jihar Kano.

Bayan tattaunawar da suka yi, jam'iyar ta amince da Salisu Takai a matsayin dan takarar gwamnan ta na jihar Kano.

Mata biyu sun samu nasara lashe tikitin APC na tsayawa takara daga jihar arewa

SanataBinta Masi wacce take daya tilo daga arewacin Nijeriya dake zauren majalisar dattawa tayi nasarar samun tikitin sake tsayawa takara domin wakiltar al'ummar yankin arewacin jihar Adamawa.

Ta samu tikitin cikin ruwan sanyi bayan rashin samun abokin takara mai neman kujerar.

Ita ma tsohuwar yar majalisar wakilai daga jihar, HajiyaAisha Dahiru, zata nemi zarcewa zuwa zauren majalisar dattawa bayan da ta lashe zaben fidda gwanin da jam'iyar APC tayi.

INEC ta hana APC fitar da dan takara a jihar Zamfara

ukumar zabe ta dauki wannan mataki na sauke yan takarar APC na jihar duba da goyon bayan kundin tsarin dokar zabe.

A cikin wani sako da kakakin hukumar, Okechukwu Ndeche, ya fitar  ma jam'iya mai mulki, hukumar tayi duba da sashi 87 da 31 na kundin zabe wajen daukar wannan matakin.

Bisa ga wannan, INEC tace jam'iyar APC bata da dan takarar gwamna da kuma yan takarar majalisun tarayya da kuma na jiha daga jihar Zamfara.

Hakan ya biyo bayan uwar jam'iyar na kasa da kuma ta jihar suka gaza cinma matsaya game da zaben fidda gwani na jihar domin tantance yan takara.

Jam'iyar ta gaza fitar da yan takarar ta kafin ranar 7 ga watan Oktoba, ranar karshen wa'adin da INEC ta bada na tura yan takarar daga jam'iyu.

Atiku ya kai ma tsohon ubangidansa, Olusegun Obasanjo, ziyara

Dan takara PDP a zaben 2019, Atiku Abubakar, ya kai ma tsohon shugaban kasa ziyara wanda a karkashin sa ya rike mukamin mataimakin shugaban kasa.

Atiku ya ziyarci Cif Olusegun Obasanjo a gidansa dake nan jihar Ogun domin neman sulhu tare da neman goyon bayan sa a zaben dake gabatowa.

Kamar yadda muka samu labari, Atiku ya isa zauren gidan Obasanjo a daidai karfe 1:05 na rana tare da wasu jiga-jigan PDP da wasu manyan malaman addini.

Cikin tawagar da suka garzaya gidan tsohon shugaban kasa akwai shugaban jam'iyar PDP, Uche Secondus, jagoran kungiyar Afenifere, cif Ayo Adebanjo, shugaban yakin neman zaben Atiku, Gbenga Daniel da Sanata Ben Murray-Bruce.

A bangaren malamai kuwa akwai Bishop Mathew Kukah, Bishop David Oyedepo da kuma Sheikh Ahmad Gummi.

Mawaki Ado Isah Gwanja ya zama ango

Shahararren mawaki kuma jarumin masana'antar Kannywood, Ado Isa Gwanja, ya shiga sahun sabbin angwaye.

An daura auren sa da masoyiyar shi Maimuna Kabir Hassan, ranar Juma'a 12 ga watan Oktoba a nan garin Kano.

Fitattun jarumai da sauran abokan aiki sa na masana'antar kanyywood sun halarci shagulgulan bikin aurensa.

Atiku ya zabi Peter Obi a matsayin mataimakin sa a takarar shugaban kasa

Bayan yan kwanaki da samun tikitin babban jam'iyar adawa ta PDP na tsayawa takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya zabi tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi a matsayin mataimakin sa.

Labarin haka ya bayana bayan ziyarar da tsohon gwamnan ya kai ma gwanin PDP a gidansa dake nan birnin taraya na Abuja ranar 12 ga watan Oktoba.