Tsohon gwamnan jihar Kano kuma dan majalisar dattawa mai zama, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yayi barazanar ficewa daga jamiyar adawa ta PDP.

Kwankwaso wanda ya fito takarar shugaban kasa karkashin jam'iyar bai yi nasarar zama gwanin PDP ba bayan da Atiku Abubakar ya samu kuri'u mafi rinjaye a zaben fidda gwani da jam'iyar tayi a Jihar Ribas makon da ya shude.

A labarin da jaridar Daily Trust ta fitar, sanatan yayi barazanar ficewa daga jam'iyar muddin uwar jam'iyar na Abuja ta cire yan akidar sa na Kwankwasiya daga cikin yan takarar ta a jihar Kano.

Jam'iyar PDP a jihar Kano ta shiga rudani ne yayin da akidar Kwankwasiiyya da na shugaban jam'iyar a jihar, Sanata Mas'ud El-jibril Doguwa, ta samu rashin jituwa game da zaben fidda gwani.

Idan ba'a manta ba a kwanan baya an gudanar da zaben fidda gwani a jihar Kano kuma yan takarar da ya fitar suka samu tikitin jam'iyar a jihar Kano.

Ita ma akidar Doguwa ta gudanar da nata zaben inda ita ma ta samu nata yan takara duk a karkashin inuwar PDP.

Sai dai uwar jam'iyar ta soke zaben da aka gudanar bayan da sauran ya'yan jam'iyar na jihar suka yi korafi kan rashin amincewar su game da zaben.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana kwamitin ayyuka na PDP ta shirya taron ne domin sasanta ya'yan jam'iyar na jihar domin cinma matsaya da zai haifar da farin ciki a cikin zukatan ya'yan jam'iyar na jihar Kano.

Labari ya kuma fito cewa shima Doguwa yayi barazanar ficewa daga jam'iyar.

Kai ga bayan kammala taron da aka gudanar game da yan takarar Kano, jam'iyar bata cinma matsaya tsakanin  yan akidar Kwankwaso da na Doguwa.