ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Sanata ya kai agaji ma wadanda riƙicin Mambila ya shafa

Sanatan ya aika da tallafin ta hanyar gidauniyyar kwankwasiyya

Sanata ya kai agaji ga wadanda rikici ya shafa

Tsohon minista na kasa kuma tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso ya aika da kayan agaji ma wadanda rikicin mambila ya rutsa da su.

Sanatan ya aika da kayan tallafin ta hanyar gidaunyyar Kwankwasiyya don amfanin yau da kullum.

A farkon watan Yuli ne riƙici ya barke tsakanin wasu kabilu a garin mambila dake karamar huƙumar Sardauna na jihar Taraba.

Sakamakon riƙicin yayi sanadiyar asarar rayuka da duƙiyoyi musamman dabbobi. Wannan ya sa wasu da riƙicin ya rutsa da su suka nemi agaji kasancewa riƙicin yayi sanadiyar sanya su a mawuacin hali.

ADVERTISEMENT

Jim kadan bayan ziyarar ganin ido da tsohon dan takarar shugaban ƙasa yayi wanda ya jajanta ma wadanda riƙicin ya rutsa da su sai gashi ya cika alkawarin da ya ɗauka na bada agaji.

Kayan sun ƙunshi burodi, shinkafa, butoci da sauran kayayyakin amfanin yau da kullum.

kwankwasso ya nuna bacin ran sa game da riƙicin kabilu da ke aukuwa a ƙasar inda yace yana ruguza zamantakewa tsakanin yan ƙasa

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT