ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Kotun koli ta wanke shugaban majalisa daga zargin da ake masa

An shigar da karar sa ne kan zargin yin karya wajen bayyana dukiyoyi da ya mallaka yayin da ya hau karagar shugabancin majalisar tarayya.

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, a zaman da alkalai biyar wanda Justice Dattijo Muhammad ya zama jagora suka gudanar kan karar ranar juma'a 6 ga watan Yuli, alkalan sun kawar da zargin da ake ma Bukola Saraki.

Hakan ya faru ne bayan da suka kalubalanci  karar da aka shigar kan rashin tabbataciyar hujja game da zargin.

A zaman da aka yi ranar juma'a, alakalan sunce hujjar da aka kaddamar gaban kotu bata kai ga zama abun lura ba saboda jita-jita ne wanda bai da tushe.

ADVERTISEMENT

Justice Centus Nweze ya karanta hukuncin da aka zartar kan karar bayan alkalan sun kawar da hujjar da aka bayyana kan zargin.

Hukuncin  ya kalubalanci matakin da kotun daukaka kara ta dauka kan karar inda masu shari'ar suka ce matakin bai kai ga hakan ba.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT