ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Kotu ta bayar da belin jarumi

Bayan kwana biyu da zaman sa a gidan kaso, mai sharia  Ravindra Kumar Joshi a ranar asabar 7 ga watan Afilu, ya bada umarni na sanya hannu ga takardar kan biyan rupee 50,000

An kama shahararren jarumin da laifin kashe wasu dabbobi yayin dauka shirin fim mai taken "Hum Saath Saath Hain" cikin shekara 1998 a garin Jodhpur.

Bayan kwana biyu da zaman sa a gidan kaso, mai sharia  Ravindra Kumar Joshi a ranar asabar 7 ga watan Afilu, ya bada umarni na sanya hannu ga takardar kan biyan rupee 50,000 kudin beli kan laifin sa bayan karar da wakilan jarumin suka shigar kan tuhumar sa.

Jim kadan bayan hukuncin, jami'an tsaro sunraka shi zuwa filin jirgi dake garin wanda ke yammacin kasar Indiya domin komawar sa ga iyalen sa.

Dandazon mabiya da masoyan fitaccen jarumin suka taru a harabar kotu domin taya shi murna.

ADVERTISEMENT

Wannan shine karo na hudu da ake shigar da karar jarumin kan laifin farautar dabba a yayin daukar shirin "Hum Saath Saath Hain". An wanke shi a kararraki ukun da aka shigar a baya.

A cikin shekarar 2006, wata kotu ta tuhumi jarumin da laifuka biyu na farauta, inda aka yanke masa hukuncin zaman gidan kaso na tsawon shekara biyar. sai dai da shekara ta zagayo, wata babbar kotu a Rajasthan, sai tayi watsi da hukuncin.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT