Pulse.ng logo
Go

Zargin wawure kudin jiha Kotu ta bada damar cigaba da garkame tsohon gwamna a kurkuku

Kotun ta bada umarnin cigaba da tsaran shi har zuwa ranar 24 ga watan Mayu bisa karar laifin wawure kudin jihar da aka shigar.

  • Published: , Refreshed:
Tsohon gwamnan jihar Filato Jonah Jang ya amshi horo a hannun jami'an EFCC play

Tsohon gwamnan jihar Filato Jonah Jang ya amshi horo a hannun jami'an EFCC

Babban kotu dake zaman ta a jihar Filato ta bada damar a cigaba da garkame tsohon gwamnan jihar, Jonah Jang a gidan kaso.

Kotun ta bada umarnin cigaba da tsaran shi har zuwa ranar 24 ga watan Mayu bisa karar laifin wawure kudin jihar da aka shigar.

A zaman kotu da aka yi ranar laraba 16 ga wata, alkali Daniel Longji ya ki amincewa da bukatar belin da tsohon gwamnan ya nema a daga ranar zantar da hukunci har sai bayan ya gama nazari kan karar shi.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta shigar da karar inda take zargin tsohon gwamnan da yin sama da fadi da makuden kudin jihar har Nera biliyan shida da miliyan dubu uku.

Hukumar EFCC tana tuhumar Jonah Jang da wawure Nera 6.3bn daga cikin zargin laifuka 12 da take yi masa da suka hada da almubazaranci da karkata kudin jama'a, cin amana da rashin gaskiya amma ya musanta dukansu.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.