ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Jamus tayi waje a gasar bana ba tare da ta tsallake daga rukunin ta

Lamarin dai ya zamanto tamkar anyi ma gasar asiri inda tun gasar 1998, kasashen da suka yi nasara na daga kofin sune kan gaba wajen fita a gasar bayan ta zagoyo ba tare da sun tsallake zuwa zagaye na biyu.

Wasan su na yanmacin ranar laraba 27 ga watan Yuni, Koriya ta doke Jamus da biyu babu ko daya.

Sakamakon bai yi ma kasar nahiyar turai dadi ba duba da yadda jama'a ke goyon bayan su na zama zakaru bayan sunyi nasarar yin haka a gasar 2014.

Da wannan sakamakon Jamus ita ce a karshen teburin ta na gasar da maki daya yayin da Mexico da Sweden suka tsallake zuwa zagaye na biyu.

ADVERTISEMENT

Hakan na nufin cewa tun gasar 1998 babu kasar da tayi nasarar kare kofin bayan ta daga ta.

Tun 1998 ga yadda kasashen suka kaya bayan zagayowar gasar:

Faransa ta ci kofi 1998

*A 2002 an fitar da Faransa a zagayen farko

*Italiya ta ci kofi 2006

ADVERTISEMENT

*A 2010 an fitar da Italiya a zagayen farko

*Spain ta ci kofi 2010

*A 2014 an yi waje da Spain tun a zagayen farko

*Jamus ta ci kofi a 2014

*A 2018 tarihi ya maimata kansa an fitar da Jamus tun a zagayen farko

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT