Tsohuwar mai suna Aisha Ibrahim ta shiga hannu jami'an ne bayan ta aikata laifin a unguwar Karaya Fulani Camp dake karamar hukumar Rafi na jihar.
Kamar yadda shaidu suka bayyana akwai rashin jituwa tsakanin tsohuwar da mahaifiyar diyar da ta kashe.
A ranar da mummunar lamarin ya faru, dan dan tsohuwar tare da matar sa sun ajiye diyar su karkashin kulawar kakar ta domin ziyartar wani taron bikin suna a wani gari dake makwabtaka da mazaunin tsohuwar. Nan ne daga bisani tsohuwar ta daure kafar diyar da igiya kana ta wurga ta cikin rijiya.
Tace tun ba yau ba tayi ma mijinta magana kan yayi ma danshi gargadi na ya tsaki matar shi amma yayi ma watsi da maganar ta. Tace surukar ta saba muzguna mata kuma hanyar da zata rama muzgunawar da ta sha a hannun ta shine matakin daure diyar cikin ta kana ta wurgar da ita rijiya.
A bayanin ta tace hakan da tayi zai koya ma uwar darasi domin ita ma taji radadin da ta ji yayin da yaron ta ya bar gidan su don komawa gare ta.
"Ina da yara 12 kuma muna zaman lafiya a gida daya, babu yadda zata zo ta ci moriyar aikin da nayi ba tare da na dauki mataki ba" tace.
Tsohuwar tayi nadamar abun da faru inda take cewa ta aikata laifin bisa halin rudani da ta shiga. Tace Allah kadai zai gafarta mata domin laifi babba ta aikata wanda mawuaci ne dan adam ya gafarta mata.
Mai magana da yawun rundunar yan sanda na jihar Niger Muhammad Abubakar ya tabbatar da lamarin tare da sanar cewa ta amsa laifin da ta aikata.
Yace za'a gurfanar da ita gaban kotu domin samun hukunci kan laifin da ta aikata bayan jami'an rundunar sun kammala bincike.