Pulse.ng logo
Go

Balarabe Musa Kashi 99 cikin 100 na mutanen dake shugabanci barayi ne - inji tsohon gwamna

Ya bayyana hakan ne yayin da amshi bakonci mawallafin jaridar Sahara Reporter Omoyele Sowore, wanda ke yunkurin tsayawa takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa

  • Published:
Buhari has failed, still Nigeria's best option - Balarabe Musa play

Former Governor of Kaduna State, Balarabe Musa

(Daily Post)

Tsohon gwamnan jihar Kaduna Balarabe Musa ya kalubalanci shugabanci a kasa, yace kashi 99 cikin na mutanen dake rike da mukamin shugabanci barayi ne.

Yace babu yadda mutum zai zama shugaba a Nijeriya idan har shi karan kanshi ba barawo bane ko kuma masu goyon bayan sa su zamanto barayin.

Ya bayyana hakan ne yayin da amshi bakonci mawallafin jaridar Sahara Reporter Omoyele Sowore, wanda ke yunkurin tsayawa takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa.

Alhaji Balarabe yace tsarin jam'iyun nijeriya da kuma lamuran gudanar da zabe na rataye ne a kan kudi, don haka yawan kudi ke ba mutum shugabancin kasa kuma ya danganci haka a matsayin yin magudi.

Ya bada misalin da shugabancin jam'horiya ta biyu wadanda ba barayi ba. A cewar shi tsohon shugaban kasa Shehu Shagari yayi mulki har ya gama bai yi sata ba wanda a yanzu ba za'a iya samun irin haka ba.

Yace rashin kyawawan tsare-tsaren tattalin arziki da na siyasa, shine dalilin rashin samun cigaban da ya kamata a Nijeriya duk da dinbim tattalin arziki da take da ita.

Tun ba yau ba tsohon gwamnan ke sukar gwamnatocin Nijeriya kan lamuran shugabanci da kuma yadda masu mulki ke gudanar da shugabancin su.

Ya sha sukar gwamnatin shugaba Shugaba Buhari kuma a baya ya soki gwamnatin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

Sai dai tsohon gwamnan bai bada kwakkwarar shaida don karfafa kalaman nasa.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.