Akalla mutum 34 suka rasu sakamakon mummunar harin da wasu yan bindiga da baa gane ko waye su suka kai kauye Gandi dake karamar hukumar Rabah ta jihar Sakkwato.

Sakamakon harin da yan bindigar suka kai ranar laraba, al'ummar garin da dama sun rasa dukiyoyin su kana wasu sunyi gudun hijira domin neman tsira.

Gwamna jihar, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal yayi Allah wadai game da harin yayin da ya halarci jana'izar wadanda suka mutu.

Gwmnan yace harin abun takaici ne tare da jaddada cewa gwamantin sa zata cigaba da taimakwa jami'an tsaro wajen kawo karshen ta'adancin yan bindiga dake neman zaman ruwan dare a jihar.

Kamar yadda NAN ta ruwaito, gwamnatin jihar ta raba kayan agaji ga wadanda sakamakon farmakin ya shafa dake nan sansanin yan gudun hijira da aka gina a karamar hukumar Rabah.

Gwamnan ya kara da cewa zai yi bakon kokarin sa wajen samar masu kayan agaji kai ga lokacin da zasu bar sansanin.

Gwamnatin jihar Sokoto ta nada wani kwamitin da zai duba abinda wadannan bayin Allah ke so, karkashin jagorancin Hon. Ibrahim Magaji Gusau, ta hukumar bada agajin gaggawa ta jihar (SEMA).

Mai shugaban kasa yace game da harin?

Shima shugaban kasa Muhammadu Buhari, yayi Allah-wadai game da harin.

A cikin wata takardar da kakakin sa, Garba Shehu, ya fitar ranar laraba 11 ga wata, shugaban yace gwamnati na iya bakin kokarin ta wajen bayyana wadanda ke da hannu game da mummunar hare-hare dake faruwa a kasar.

Yace abun takaici ne yadda kangararrun yan ta'adda ke far ma jama'a wadanda basu san hawa balle sauka.

Ya sha alwashin cewa gwamnati zata kawo karshen kashe-kashen dake faruwa tare da bayyana wadanda ke goyon bayan ta'adancin.

Daga karshe shugaban ya mika sakon ta'aziya ga iyalen wadanda rikicin ya shafa da gwamnatin jihar Sakkwato.