Pulse.ng logo
Go

Azumin bana Kasashen da zasu fi shan wahalar azumin watan Ramadan

Yayin da kasar Nijeriya da wasu kasashen nahiyar Afrika ke daukar misalin sa' o' i 14 kafin su karya azumi, lamarin ya bambanta a wasu kasashe duniya.

  • Published:
Top European football clubs wish their Muslim fans a blissful Ramadan play

Barka da shigowa watan Ramadan

(comingsoon)

Musulmai kimanin biliyan biyu sunĀ  wayi gari a kasashe daban daban na duniya da azumin farko na watan Ramadan na bana.

Wannan ya biyo bayan ganin jinjirin watar ramadan wanda ya tabbatar daukar azumi.

Yayin da kasar Nijeriya da wasu kasashen nahiyar Afrika ke daukar misalin sa' o' i 14 kafin su karya azumi, lamarin ya bambanta a wasu kasashe duniya.

Ba wani abu ya janyo hakan face bisa lamarin yanayin faduwar rana da fitowar alfijir.

Ga kasashen da kuma lokatan da suke dauka tsakanin sahoor da bude baki:

Iceland

Shine kasar mai dogon zango kafin a sha ruwa. Musulman kasar zasu yi azumi na tsawon awa 20 kafin a sha ruwa. Alfijir yana ketowa kafin karfe 2 na dare kuma ana yin bude baki karfe 12 na dare

Kasar Rasha

Mutananen kasar zasu yi awa 20 suna azumi. Ana daina cin abinci karfe 1:30 na dare kana a bude baki karfe 9 na dare.

Norway

Nan ma awa 20 musulman kasar zasu yi suna azumi. Alfijira ya kan keto karfe 2:00 na dare kana a bude baki karfe 10:30

Ingila

Awa 19 suna azumi. Ana daina cin abinci karfe 3:00 na dare kana a bude baki karfe 9 na dare.

Netherlands

Awa 19 suna azumi. Ana daina cin abinci karfe 3: 00 na dare kana a bude baki karfe 10 na dare.

Kasashe irin su Argentina da Australia na da lokata kadan fiye da sauran kasashe na yin azumi. Sa'o'i 11 musulman kasar zasu yi da azumi.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement