Kano ta samu sabon 'Dan masanin Kano'
Alhaji Abdulkadir Maitama Sule ya gagi sarautar ne daga mahaifin shi wanda ya rasu cikin watan Yuli na shekarar 2017.
Masarautar Kano ta nada Alhaji Abdulkadir Maitama Sule da sarautar a karshen makon da ya shude.
Ya gaji sarautar ne daga mahaifin shi wanda ya rasu cikin watan Yuli na shekarar 2017.
Marigayi, Dakta Yusuf Maitama sule ya rasu a ƙasar masar inda ya yi jinyar rashin lafiya da yake fama da ita a safiyar litinin 3 ga watan Yuli.
Dan masanin kano shahararren dan siyasa ne wanda ya rike mukamin minista kuma yayi takarar shugaban kasa a jam’iyar NPN a shekara 1979.
Ya rasu yana da shekaru 87 a duniya
JOIN OUR PULSE COMMUNITY!
Eyewitness? Submit your stories now via social or:
Email: eyewitness@pulse.ng