ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Kalli jerin yan wasa 7 da muke sa ran cewa zasu maye gurbin fitattun jarumai a 2018

Manyan gobe da zasu zama idon jama'a a masana'antar nishadantarwa ta kannywood cikin 2018

Wannan dandalin ta cigaba da bunkasa martaban arewan ta hanyar wasanni don nishadantarwa da fadakar da jama'a da labarurruka masu kayatarwa.

A cikin shekara ta 2017 Kannywood ta samu canji ko kuma ince ta fara sauya yadda aka saba ganin fina-finan ta sanadiyar kaddamar da tsarin Box office wanda zai taimakawa wajen haska fina-finai a sinimomi da gidajen kallo.

Hakazalika masu ruwa da tsaki na masana'antar sun gyara fuskar yadda suke shirya fina-finai inda a halin yanzu suna takama da kayan aikin fasahar zamani wajen shirya fim.

ADVERTISEMENT

A 2017 kannywood ta samu wasu sabbin jarumai tare da tsoffin jarumai matasa wadanda tauraron su ke haskawa

Ga wasu cikin su muna iya cewa sun shigo masana'antar da kafar dama yayin da sauran ke jajircewa wajen bayyana basirar su bainar jama'a.

Ga jerin jarumai wanda muke ganin cikin 2018 gwanintar su da kuma nuna fasahar su zai janyo haske ga tauraron su a masana'antar.

Munyi masu lakabi da "Manyan Gobe";

1. Maryam Yahaya

ADVERTISEMENT

Bana wannan jaruma tana sahun gaba cikin jarumai da tauraron su ya haska.

Bayan fitowar ta shirin "Mansoor" ta cigaba da nuna mana irin basirar dake tattare da ita wanda suma masu shiryawa fina-finai suka shaida hakan har ma suke ta haska ta a fina-finai daban daban.

2. Rashida Lobbo

Bana dai wannan jarumar ta samu kyautar a jihar legas bisa ga rawan da ta taka a masana'antar Kannywood.

3. Amal Umar

ADVERTISEMENT

Amal tana cikin yan wasa da suka yi fice acikin shirin MTV "shuga" wanda ake yi cikin harsheb turanci. Banda haka jarumar ta fito a fina-finai da dama na masana'antar kannywood.

4. Umar M.Sheriff

Fitaccen mawaki Umar M.Sheriff ya gwada iyawan shi fitowaer shi a cikin "mansoor" a matsayin jarumi kuma da alama ya ji dadin hakan kuma zai cigaba da damawa a cikin harkar.

5. Halima Ibrahim

Jarumar ta fito a cikin shirin "Rabu da Maza" tare da fitaccen jarumi Sadiq Sani Sadiq da kuma jaruma Amal Umar

ADVERTISEMENT

6. Garzali Miko

Shima dai wannan mawaki yana tafarkin sauya sheka zuwa fannin fim.

7. Ahmad Illiyas Tantiri

Ahmad daya daga cikin yaran babban direkta kuma mai shirya fim ne watau Abdulmumin Illiyas Tantiri.

Yana daya daga cikin yara dake kokartawa a farfajiyar fim.

ADVERTISEMENT

Ga jaruman bana shekara ce na shirya damawa da sauran fitattun jarumai.

Yayin da muke shirin shiga wata sabuwar shekara na 2018, da fatan dai zasu kokarta a cikin ta.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT