ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Fitattun Fina-finai Hausa 5 da ya kamata ku kalla

Dukaninsu a fitar dasu cikin bana kuma suna dauke da labari mai fadakarwa

Masana’antar kannywood ta shirya damawa da sauran masana’anta shirya fim.

Tun farko shekara ake sako sabbin fina-finai mai dauke da sabon labari kuma mai fadarkawa, ilimantarwa kuma mai koya darasi.

Ga wasu shirin fim 5 da ya kamata ace kun kalla.

An shirya su ne da fitattun jarumai wadanda suka kware a harkar kuma tsare-tsaren da aka bi wajen fitar dasu yana da yawa.

ADVERTISEMENT

Jaruman sun taka rawa sosai a cikin shirin hakazalika masu wadanda suka shirya su tare da masu bada umarni sun nuna kwarewar su wajen fitar da fina-finan.

Suma marubutan sun taimaka da basirar su wajen rubuta fina-finan.

Ga fina-finan kamar haka;

1.RARIYA

Jaruma Rahama Sadau ta dauki nauyin fitar da wannan shirin kuma Yaseen Auwal ya bada umarni.

ADVERTISEMENT

2. Kalan dangi

Ita ma jaruma Aisha Aliyu Tsamiya ta shigo sahun sauran jarumai masu daukan nauyin shirin fim. Shirin wanda Ali Gumzak ya bada umarni ya samu fitattun jarumai irin su Ali Nuhu, Sadiq Sani Sadiq, Aminu Sheriff Momo, Hafsat Idris da sauran su.

3. Mansoor

Hakika kowa yaba wannan shiri wanda sabuwar tauraruwar fim Maryam Yahaya tare da Mawaki Umar M.Sheriff suka haska a ciki. Jarumi mai kwazo Ali Nuhu ya bada umarni a shirin.

4. Rumana

ADVERTISEMENT

Kamfanin hikima multimedia ta dauki nauyin fitar da wannan shirin wanda Rahama Sadau, Adam A.Zango, Aminu Sheriff Momo suka taka rawa a cikin ta. Ali Gumzak ya bada umarni.

5. Kujerar wuta

Dalilin da zaka so ka kalli wannan shirin shine akwai tsohuwar tauraruwa Hauwa Maina a ciki kuma ta nuna kwarerta a harkar fim. Halilu umar ya dauki nauyin shirin.

Kuna iya zuwa kallon su a sinima ko ku tuntubi yan kasuwa domin samun su.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT