Leftana Kanar Ali ya rasu wajen yaƙi da ʼƴan taʼada-Boko Haram. An yi wannan kyauta a ranar 4 ga watan Nuwamba, 2016.
Gwamnan Borno ya bá da kyauta na N10 miliyan ga iyálin Soja wanda aka kashe
Gwamnan Borno ya saƙa ma iyali na marigayi LeftanaKanar Abu Ali da kyautan ƙudi N10 miliyan.
Gwamna Kashim Shettima, yá yi wannan kyauta a lokacin da ya kai gaisuwa wajen gwauruwan marigayi.
Malam Isa Gusau, babban mashawarcin Gwamna ga harkokin sadarwa da dabarun, ya yi wannan kalami a Birnin Maiduguri.
Á cikin kalamai, Gwamnan Borno ya miƙa kuɗin takarda N10 miliyan ga Samira, waton Gwauruwan Soja mai karfin zuciya, wanda ya rasu.
Marigayi Leftana Kanar Ali, ya rasu a garin Malam-fatori, babban birnin ƙaramin hukumar Abadam a Jihar Borno Ya rasu a ranar 4 ga watan Nuwamba, 2016.
Shettima ya bayyana cêwa marigayi Soja Ali, gwarzo ne wanda yá hadaya rayuwarsa domín zaman lafiya na mutanen Jihar Borno, Arewa ta Gabas, da kuma Najeriya gaba ɗaya.
Ya yi adduʼa ga Allaha (SWA) ya yi masa rahama, ya kuma jiƙansa.
Shettima ya ɗauki ɗan lokaci domin muʼámala da uwar marigayi da kuma yaransa, domin tabbatar musu cêwa hadayat na marigayi Ali ba zai zama aikin banza.
JOIN OUR PULSE COMMUNITY!
Eyewitness? Submit your stories now via social or:
Email: eyewitness@pulse.ng