Harkar siyasa da yakin neman zaben ya mamaye kasar inda yan takara na jamiyu mabambanta dake fadin kasar ke neman cinma burin su na shugabanci.

Bisa ga wannan yanayin da ake ciki tawagar ma'aikatan yakin neman zaben shugaba Muhammadu Buhari ta fitar da wasu kayayatattun hotunan shugaban bayan jam'iyar APC ta amince da tsayawar shi.

Kai ga yanzu shugaban shine gwanin jam'iya mai mulki, yayi nasarar zama dan takarar ta bayan da ya samu kuri'u 14,842,072 daga deliget na jam'iyar.

APC ta tabbatar da haka a taron kasa da ta gudanar ranar Asabar 6 ga watan Oktoba a filin Eagle square dake nan birnin tarayya.

Shugaban zai kara da Atiku Abubakar na jam'iyar PDP da yan takarar sauran jam'iyu wajen zarcewa a saman kujerar mulki a zaben 2019.

Tsohon mataimakin shugaban kasa ya doke sauran yan takarar PDP wajen zama gwanin jam'iyar bayan zaben da aka gudanar a garin Fatakwal karshen makon da ya gabata.