Pulse.ng logo
Go

Jarumar Kannywood Kalli kayatattun hotunan Saratu Daso da mijinta

Jarumar wanda ta fiye fitowa a matsayin matsayin muguwa ko mai azabtarwa a cikin fina-finai hausa ta wallafa hotunan ne a shafin ta na dandalin sada zumunta inda take nuna farin cikin ta ga rayuwar auren su.

  • Published:
Jaruma tare da maigidanta play

Jaruma tare da maigidanta

(Instagram/saratudaso)

Shahararriyar jarumar Kannywood kuma daya daga cikin iyayen masana'antar Saratu Gidado wanda aka fi sani da Saratu Daso ta fitar da hotunan ita da mijinta.

Jarumar wanda ta fiye fitowa a matsayin muguwa ko mai azabtarwa a cikin fina-finai hausa ta wallafa hotunan ne a shafin ta na dandalin sada zumunta inda take nuna farin cikin ta ga rayuwar auren su.

play (Instagram/saratudaso)

Cikin sakon da ta fitar bayan saka hotunan jarumar ta rubuta "Ustazai ne mu fa". Hotunan dai sun birge inda masoya masu bibiyan shafin ta suka ta kwararo masu addu'a.

A cikin wani hoton da ta sake wallafawa, jarumar ta rubuta "ku cigaba da kwararo mana Addu'a".

play (Instagram/saratudaso)

 

Saratu Gidado tana daya daga cikin jarumai mata masu harkar fim duk da auren su. A wata hira da tayi kwannan baya, tace mijinta yana mara mata bisa aikin fadarkarwa da yan fim keyi kuma bata taba nadamar aikin da take yi.

A cewar ta tana tsare mutuncin aurenta kuma tana fim kamar yadda sauran mata ke tafiyar da aikin su a ma'aikata da dama da ma masu aikin sana'ar hannu na yau da kullum.

Ta kara da cewa mai gidan ta baya jin komai ganin yanayin rawan da take takawa a fim na fitowa a matsayin mugunta domin ya san cewa wasan kwaikwayo ne.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement