Pulse.ng logo
Go

Mutuwar Sheikh Imam Lawal Kalli dandazon jama'a da suka halarci jana'izar babban malami

Anyi jana'izar shi a babban fili dake nan wajen kofar fadar sarkin Katsina da misalin karfe 2:30 na rana

  • Published:
Dandazon jama'a a wajen jana'izar Sheikh Imam Lawal play

Dandazon jama'a a wajen jana'izar Sheikh Imam Lawal

(Facebook/rariya)

Dandazon jama'a suka halarci sallar jana'izar limamin babban masallacin Katsina wanda ya rasu ranar Lahadi.

Limamin,  Sheikh Imam Lawal ya rasu a safiyar ranar lahadi 6 ga watan Mayu a gidan sa dake nan unguwar liman.

Dandazon jama'a a wajen jana'izar Sheikh Imam Lawal play

Dandazon jama'a a wajen jana'izar Sheikh Imam Lawal

(Facebook/rariya)

 

Anyi jana'izar shi a babban fili dake nan wajen kofar fadar sarkin Katsina da misalin karfe 2:30 na rana.

Anyi jana'izar shi a harabar dake wajen kofar gidan sarkin Katsina play

Anyi jana'izar shi a harabar dake wajen kofar gidan sarkin Katsina

(Facebook/rariya)

 

Limamin ya rasu yana da shekaru 95 a duniya.

Shima shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon ta'aziyar sa ga iyalen sa.

A cikin takardar da kakakin sa Garba Shehu, ya sa hannu, shugaban yayi jimamin mutuwar marigayin. Yayi kira na a koyi kyakkyawar halayen marigayin kasancewa ya gudanar da rayuwar sa cikin saukin kai.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.