ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Kakakin majalisar wakilai yace babu wanda zai hana shi takara

Ya fadi hakan ne yayin da wasu magoya bayan sa daga mazabar sa suka ziyarci gidan sa dake nan birnin tarayya ranar Talata 11 ga wata.

Ya kara da cewa ba zai daina tsayawa takara ba sai ya kammala ayyukan cigaba da yake yi ma kasa.

A cikin sakon da ya wallafa a shafin sa na Tuwita, jagoran majalisar wakilan tarayya yace zai tsaya takara bayan amincewar al'ummar mazabar sa.

Bugu da kari yace zai tsaya takara don ya karya mutanen dake neman yi masa ritaya.

ADVERTISEMENT

Da alama ya mayar da da raddin ne ga gwamnan jihar Bauchi da Bola Tinubu wandanda ake ganin sun samu rashin jituwa bayan yayi nasarar zama kakakin majalisa.

Yakubu Dogara yana wakiltar al'ummar yankin Bogoro/Dass/Tafawa Balewa na jihar Bauchi ya shiga zauren majalisar tarayya tun cikin shekarar 2007.

Duk da cewa ya jaddada cewa zai sake tsayawa takara a zaben 2019, kakakin bai sanar da jam'iyar da zai fito takara karkashin ta.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT