Pulse.ng logo
Go

Jullen Lopetegui Real Madrid ta sanar da jagoran Spain a matsayin sabon kocin ta

Sabon kocin zai fara aiki bayan kammala gasar cin kofin duniya inda yake jagorantar kasar Spain

  • Published:
Julen Lopetegui sacked as Spanish coach after Real Madrid appointment play

Sabon jagpran kungiyar Real Madrid, Jullen Lopetegui

(The sun)

Tawagar kungiyar Real Madrid ta sanar da Jullen Lopetegui a matsayin wanda zai maye gurbin tsohon jagoran ta.

Zakarun turai na bana sun sanar da haka ne kwana uku gabanin fara gasar duniya a kasar Rasha.

Sabon kocin mai shekara 51 ya sa hannu ga yarjejeniyar na shekara uku wanda zai fara bayyana kammala gasar cin kofin duniya kasancewa shine wanda ke jagorantar kasar Spain a gasar.

 

Tsohon kociyar tawagar Porto ya shiga mahangar Madrid bayan da Zinedine Zidane yayi murabus cikin watan Mayu.

Jullen Lopetegui ya taka leda da Madrid sanda yake matashi a matsayin mai tsaron raga. Hakazalika ya kuma jagorantar tawaga ta biyu na kungiyar shekarun baya.

Sabon kocin ya maye gurbin Vicente del Bosque wajen jagorantar kasa Andalus cikin shekarar 2016 bayan tsohon jagoran yayi nasara lashe gasar kofin duniya a 2010 da kofin nahiyar turai a shekarar 2012.

 

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.