Kwamishinan lafiya, Likita Balarabe Kakale ya bayyana a ránar Lahadi da yake tattaunawa da Hukumar ʼƳan Jaridan Najeriya (NAN) a birnin Sakkwato.
Kakale ya bayyana cêwa an ɗauki wannan mataki domín a rage nauyín aiki wanda maʼaikatan Asibitin Jihar da na Jamiʼar Usmanu Danfodiyo suke fama da shi. Da yake bayani, ya cé:
"Maʼaikatan lafiya wanda aka dirka sun ƙunshi likitoci ashirin, maʼaikatan aikin jinya da unguwar zoma ɗari da hamsin da biyar.”
“Ba mu haɗa da sauran maʼaikaci masu kula da lafiya waɗanda suna wurare kamar asibitin unguwa da maʼaikata masu bi gida zuwa gida.
"A takaice, waɗanan maʼáikatan da aka dirka, ba zasu sauya maʼaikatan cibiyoyin lafiya. Za su ƙara musu ƙarfin gwiwa ne”.
Kwamishana ya ce, án ɗauki wannan mataki domín a kawo cibiyoyin lafiyá kusa da jamaʼa, da kuma tabbatar da cewa án gudanár da allurai riga-kafi, domin kula da lafiyan masu ciki da kuma ƙara ƙarfin ƙananan cibiyoyi masu kula da lafiyan jiki.
Kamar yanda ya yi bayani, kwamishana ya cé waɗanan cibiyoyin kula da lafiya suna da ƙarfin aiki. Ya ce:
“Waɗanan cibiyoyi suna da umarnin kula da matsaloli masu sauƙi. Suna damar kula da masu ciki, ciwon zazzabi na sauro, tabbatar da cewa án bi doka na duba gari, miƙa babban matsololi zuwa babban asibiti da sauran ayyuka.