Mataimakin gwamnan jihar Kano Farfesa Hafiz Abubakar ya dauki matakin ajiye mukamin sa a gwamnatin jihar bisa wasu dalilai na rashin tsakanin sa da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje.

Tsohon mataimakin gwamnan ya mika takardar murabus dinsa ne ranar lahadi.

Tunda ba yau ba mataimakin gwamnan da gwamnan ke takun tsaka sanadiyar rashin daidaituwa a fannin siyasa. Tsohon mataimakin sanannen dan hannun daman tsohon gwmnan jihar ne kuma dan akidar kwankwasiya ne.

Kamar yadda takardar ta nuna Farfesa Hafiz ya ajiye aikin sa bisa wadannan dalilai

An mayar dashi saniyar ware

tsohon mataimakin yace wata sayi da kudin aljuhun sa yake gudanar da wasu ayyukan gwamnati. Yace ana tauye hakkin shi wajen fitar da kudaden alawus na tafiye-tafiye.

Barazana ga rayuwar sa

Gabanin mika takardar ajiye aikin da yayi, tsohon mataimakin gwamnan ya shaida wa BBC cewa shi da gwamnan suna zaman doya da manja saboda yana tare da tafiyar Kwankwasiya kuma lamarin ta kai ga yi ma raywarsa barazana.

Kokarin hana hatsaniya bata yi nasara ba

A cikin wasikar da ya tura ma fadar gwamnatin jihar, Farfesa Hafiz yace ya sha jan hankalin gwamna game da wasu batutuwa dake iya tada husuma a siyasar jihar sai dai kuma kuma kokarin nasa bata yi nasara ba.

Kokarin tsige shi daga mukamin

A cikin wata sanarwa da kwamishnan watsa labarai na jihar Muhammed Garba ya fitar, gwamnatin jihar tace tsohon mataimakin ya ajiye aikin sa ne yayin da majalisar jihar ke kokarin tsige shi.

Yan majalisa 30 cikin 40 suka sa hannu ga kudurin tsige shi kan zargin da ake masa na yi ma gwamnatin jihar zargin karya.

Martanin gwamnatin jihar Kano

Gwamnatin jihar ta mayar masa da martani bisa zarge-zargen da yayi inda tace babu wata tsabani da aka samu daga bangaren gwamna Ganduje. A cikin sanarwa da Kwamishnan watsa labarai na jihar yayi, gwamnati ta musanta zargin da yayi na cewa ana tauye hakkin sa wajen kudadaden alawus.

Gwamnatin tace ko a cikin shekarar 2017 naira miliyan 120 aka kashe wa ofishin mataimakin gwamnan na kudin aluwus na tafiye-tafiye. Bayan haka an kashe sama da miliyan 30 a wannan shekarar na kudin alawus na tafiye-tafiyen sa.

Daga karshe gwamnatin ta musanta zargin da yayi na cewa gwamnatin jihar ta ware kudin na musamman domin gudanar da gangami a kan ya ajiye mukamin sa. Kwamishnan yace wata kila gwamnati ta kai kara kotu kan zargin da yayi.