Pulse.ng logo
Go

Sani Mu'azu Jihar filato zata karrama shahararen jarumi

Sani Mu'azu ya farin cikin sa bisa karramawar da za'ayi masa a wata sanarwa da ya wallafa a shafin sa na facebook tare da sanya hoton shi kamar yadda kungiyar ta fitar tare da jadawalin ranar bikin

  • Published:
Sani Mu'azu play

Sani Mu'azu

(Facebook/sani muazu)

Wata kungiyar mai girmama yan kasar Filato na shirin karrama shahararren jarumin Kannywood Sani Mu'azu.

Kungiyar mai suna Plateau man of the year Awards cikin shirin ta na girmama manyan mutane yan jihar Filato da suke taka muhimmin rawa a fannoni daban daban don cigaban jihar, zata girmama jarumin bisa gudummawar sa ga cigaban harkar nishadantarwa a jihar.

Za'a girmama shi bisa gudunmawar da yake bada wa a bangaren nishadantarwa don cigaban jihar play

Za'a girmama shi bisa gudunmawar da yake bada wa a bangaren nishadantarwa don cigaban jihar

(Facebook/sani muazu)

 

Sani Mu'azu ya farin cikin sa bisa karramawar da za'ayi masa a wata sanarwa da ya wallafa a shafin sa na facebook tare da sanya hoton shi kamar yadda kungiyar ta fitar tare da jadawalin ranar bikin.

Za a yi bikin karramawar a ranar 23 ga Afrilu, 2018 a otal ɗin The Crest Hotel da ke Jos.

Jarumin, yana daga cikin tsofafin jarumai da suka raya masa'antar Kannywood. Shine kashin bayan kafa hadaddiyar kungiyar masu shirya fina-finai (MOPPAN).

Yana daga cikin jaruman kannywood da suke taka rawar gani a nollywood, ya fito a cikin fina-finan turanci da dama na masana'antar dake kudancin Nijeriya.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.