Sojoji sun kamá wani maƙaryaci mai kiran kansa soja
An kama wani mayaudarin mutane mai farantin kansa a matsayin soja a yayin da zai sayar da wayan tarho wanda ya sace.
A cikin ƙarshen mako wanda ya wuce, ʼƴan jaridan Daily Post sun kawo rahoto cewa sojojin birged na manyan bindigogi, sun kama wani Adam Alexander mai shekara ashirin da biyu, a lokacin da yake koƙarin sayar da waya wanda ya sace.
ʼƳan jaridan Daily Post, sun yi rahoto cewa an kama wannan matashi a lokacin da yake farantin kansa cikin kayan sojoji.
Mataimakin Darektan labaru na Sojoji, Kyaftin Sunday Akinkumi, ya bayyana cewa wannan matashi yana amfani da kayan sojoji domín aikatawa laifuka kamar fashi da taʼadanci.
Kamar yanda ya yi bayani, Akinkumi ya ce wannan maƙaryaci ɗan Maiduguri ne, a jihar Borno. Ya ce:
"An kama shi a kasuwan wunti sanye da kayan soja na ƙarya. Yana koƙarin sayar da tarhon Samsung Galaxy Note 5 wanda ya sace.
"Ya sa farashe naira dubu sabaʼin (N70,000).”
Za á gurfanar da shi a gabán kotu a cikin lokaci.
JOIN OUR PULSE COMMUNITY!
Eyewitness? Submit your stories now via social or:
Email: eyewitness@pulse.ng