ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

ʼƳan wasan kwaikwayon Nollywood wanda ya kamata ku lura da su a 2017

Ina ʼƴan wasan kwaikwayon Hollywood wanda kuke ji da su a wannan shekara na 2017? Ku lura da waɗannan biyar. Mun lissafa su ba tare da tsari.

Somkele Idhalama, Seun Ajayi and Rahama Sadau

A kowane shekara, a kan samu sabbin tauraro a Nollywood. Haka ma a cikin shekara na 2016, mun gani sabon tauraro kaman Rahama Sadau, Somkele Idhalama da Judith Audu.

Daga duk alama, shekara na 2017 ya nuna yiwuwar shekara mai kyau sossai, kuma mun shirya muku jerin ƴan wasan kwaikwayo waɗanda muke sauraransu a cikin shekara na 2017.

A cikin shekara na 2016, waɗanan ƴan kwaikwayo sun aiwatar da wasanni masu fice. Saboda ayyukansu, da wassaninsu masu shaʼawa, masoyan kwaikwayo sun sa musu ido domin ganin aikin da suke shiryawa.

Ga ƴan wasan kwaikwayo wanda muke lura da su a shekara 2017 ba tare da tsari:

ADVERTISEMENT

1. Greg OJ- Greg OJ ɗan wasan kwaikwayo ne wanda ya nuna gwaninta a shekara na 2016. Lambar yabon ƴan wasan kwaikwayo na Africa Magic sun zaɓe shi domin fitowansa a cikin wasannin "Itʼs Her Day", "Just Not Married", "Room 315", "Arbitration", da "Suru Lere". Ya karɓi lambar yabo a 2016. Zai fito cikin shirin Stanlee Ohikhuare mai suna "Behind the Wheels".

2. Rahama Sadau- A cikin shekara na 2016, Ƙungiyar masu hotó da wasaʼn Ƙwaikwaiƴo sun dakatar da Rahama daga Kannywood domin wasan da ta yi tare da ClassiQ, wani mawaƙi wanda yake garin Jos. Bayan wannan, Rahama ta zama shahararra.

A cikin watan Oktoba na shekaran 2016, Bayan an dakatar da Rahama, Jeta Amata da Akon sun gayyace ta zuwa Hollywood, domin yin sabon fim mai suna "The American King".(Waton "Sarkin Amirka").

Bayan haka, Rahama ta fito ga shirin Kamfanin Ebony Tv. Sunan shirin shi ne "Sons of the Caliphate" wanda ta taka rawar ʼBintaʼ.

Rahama za ta fita cikin finafinan Hollywod kaman "Hakkunde", "Ajuwaya", "Light will Come", da kuma "Sons of the Capliphate 2". Rahama za ta saki sabon bidiyo mai suna "Rariya" wanda ta yi.

ADVERTISEMENT

3.Somkele Idhalama- Wannan ƴar wasa ita ce sabon ƴar wasa, tauraro mafi-girma wanda ya fito a Hollywood a shekara 2016. Somkele ta taka rawar uku cikn manyan finafinan shekara 2016: waton "The Arbitration", "93 Days" da kuma "The Wedding Party". Waɗannan finafinai sun ci lambar yabo. Somkele ta samu lambar yabo biyu domin rawar wanda ta yi a "93 Days".A cikin shekara na 2017, Somkele  za ta fita a shirin "The Guest" da "Ojukokoro".

4.Judith Audu- Wannan ƴar wasa ta samu ci gaba a cikin shekara na 2016. Ta yi farkon fita cikin bidiyo na sinima, kuma ta fito cikin finafinai shida. Ta fito cikin "Romance is Overrated", "Deeply Cut", "Just Not Married", "Gone Gray", "Colourless", da kuma "Yes, I Donʼt".

Ta karɓi lambobin yabo da yawa domin taka rawan da ta yi na "Keji". A cikin shekara na 2017, za ta fito cikin "Hakkunde", da "Just Before I do" da kuma wasu sauran wasanni.

5.Seun Ajayi- Ɗan wasan kwaikwayo mai suna Seun Ajayi ya bambanta kansa da mussaman a cikin wasan "Suru Lʼere" a inda ya taka rawar Arinze. Yana cikin ƴan wasan da ya kamata a lura da shi a Nollywood cikin shekara na 2017. A shekara na 2016, ya fito cikin shirin "Hustle" da kuma "93 Days".

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT