ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Babu abun da ya shiga tsakani na da Adam A.Zango kana na daina fitowa a matsayin dan daudu

Jarumi  wanda ya shahara wajen fitowa a matsayin dan daudu a fim, ya bayana cewa zai daina fitowa a matsayin haka

Jita-jitra dake yaduwa a kafafen sada zumunta na cewa jarumai suna takun saka tsakanin su.

Hirar shi da jaridar Premium Times, Ado Gwanja yayi karyata jita-jitan tare da bayana hakikanin alaka dake tsakanin sa da tauraron Kannywood.

Yana mai cewa " Kasan ba a rasa wadanda basu rasa abin cewa a kullum. Su bi wurare suna fetsa maganganu iri-iri. Amma ni dai a sani na babu abin da ya shiga tsakani na da Adam Zango. Hasali ma shi maigida na ne domin ni a yaron sa na fara sana’a ta kuma har yan zu ma haka ne.

Jarumi  wanda ya shahara wajen fitowa a matsayin dan daudu a fim, ya bayana cewa zai daina fitowa a matsayin haka. Yace daga yanzu matsayin barkwanci kawai zai dinga fitowa a cikin fina-finai.

ADVERTISEMENT

" A’a yanzu kam na dai na fitowa a fina-finan da zai haska ni a matsayin dan daudu. Zan tsaya a barkwanci na kawai" yace.

Yayi ma dinbim masoyan sa godiya bisa soyayar da suka nuna masa game da wakokin sa kana yana masu albishiri cewa zai cigaba da nishadantar dasu.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT