Pulse.ng logo
Go

Mc Ibrahim Sharukan Jarumi ya zama ango, kalli hotunan daurin auren shi

An daura auren shi ga amarya Halima Shehu Usman ranar asabar 5 ga watan Mayu a  garin Kano

  • Published:
baki a wajen daurin auren Mc Ibrahim Sharukhan play

baki a wajen daurin auren Mc Ibrahim Sharukhan

(Instagram/mlmibrahimsharukhan)

Shaharraen jarumi kuma mai gabatar da shirye-shirye a wajen taron biki, Mc Ibrahim Sharukan ya zama ango.

An daura auren shi ga amarya Halima Shehu Usman ranar asabar 5 ga watan Mayu a  garin Kano.

Uzee Usman tare da ango Mc Ibrahim Sharukhan play

Uzee Usman tare da ango Mc Ibrahim Sharukhan

(Instagram/mlmibrahimsharukhan)

Jarumin ya sako hotunan taron daurin aure wanda ya dauka tare da sauran abokan sa da suka halarci taron, a shafin sa na kafar sada zumunta ta Instagram.

Taron daurin auren ya samu halartar yan uwa da abokan arziki ciki har da wasu manyan kusoshin masana'antar kannywood da jarumai.

Cikin manyan jarumai da suka halarci daurin auren akwai, mai shirya fim Aminu Saira da jarumi Yakubu Muhammed da Uzee Usman da mawaki Nazifi Asnanic.

Jaruman kannywood a wajen daurin auren Mc Ibrahim sharukan play

Jaruman kannywood a wajen daurin auren Mc Ibrahim sharukan

(Instagram/mlmibrahimsharukhan)

A makon da ya gabata aka shirya kayatattun bukukuwa  wanda ya kwashi kusan mako daya ana bikin.

Ango tare da baki a wajen daurin auren jarumi play

Ango tare da baki a wajen daurin auren jarumi

(Instagram/mlmibrahimsharukhan)

 

An shirya wasannin da dama na raya auren sa. Jarumai da dama sun halarci tarurukar bikin auren kuma da bisa ga hotunan da ke ta yawo a kafafen sada zumunta, bukukuwan sun kayatar matuka.

Daga nan sashen hausa na Pulse muna masafatan alheri, Allah ya bada zaman lafiya.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.