Wani matashi mazaunin garin Abuja mai suna Nurudeen Iliyasu ya matakin  sadaukar da ransa domin nuna bacin ransa game da halin yunwa da kasa ke ciki.

Matashin mai shekaru ashirin da takwas ya hau falwayan kamfanin sadarwa ta Airtel dake nan kusa da fadar shugaban kasa duk cikin matakin na ganin cewa shugaban ya sauka daga mulki duba da halin da yan kasa ke fuskanta.

Lamarin ya faru a ranar laraba 12 ga wata inda matashin ya hau zuwa kololuwar falwayan da niyar sadaukar da raywar shi domin ganin an samu gyara a kasa.

A cikin wata wasika da ya bari gabanin hayewar sa Iliyasu ya sanar cewa yana zanga-zanga na kin cin abinci na tsawon kwana bakwai kuma bai da niyar sauka daga falwayan har sai bayan shugaba Buhari yayi murabus kuma ya ajiye aniyars na zarcewa zuwa wa'adi na biyu a saman mulki.

Sai dai amma bayan sa'o'i 24 Iliyasu ya sauka bisa ga yarjejeniya da ya samu da jami'an tsaron na yin magana da manema labaru.

Bayan saukar sa, Nurudeen Iliyasu ya shaida ma manema labarai dalilin daukar matakin da ya dauka don nuna adawar sa da gwamnatin shugaba Buhari.

Yayi koka kan halin yunwa da kasar ke ciki tare da nuna rashin goyon bayan anniyar shugaban na sake shugabantar kasar.

A cewar shi bai dace shugaban ya kara wa'adi na biyu a karagar mulki bayan zaben 2019. Yace ya kamata shugaban ya mika wuya ya fadi a zaben domin baiwa yan takarar sauran jam'iyar damar mulki.

Daga karshe ya jaddada cewa ba ya fama da wata cuta ko kuma tabin hankali sabanin yadda wasu ke yi masa lakani.