Pulse.ng logo
Go

Jarumi sadauki Jami'i wanda ya nuna jaruntakar shi wajen kama gawurtaccen mai garkuwa da mutane Evans ya gamu da ajalin sa a fagen yaki

An harbi sajent Lanre Sanusi a ciki yayin da yake kokarin kama wasu masu garkuwa da mutane.

  • Published:
Marigayi Sajent Lanre Sanusi play

Marigayi Sajent Lanre Sanusi

Jarumin dan sanda da ya taimaka wajen kama gawurtaccen mai garkuwa da mutane Evans ya gamu da ajalin sa.

An harbi sajent Lanre Sanusi a ciki yayin da yake kokarin kama wasu masu garkuwa da mutane.

Rahoto ya nuna cewa an harbe shi a ciki tare da abokin aikin sa wanda aka harba a kafa.

Duk da harbin da aka yi masa wannan jarumin dan sanda tare da abokan aikin sa sun cigaba da bin masu garkuwa har suka samu damar kashe wanda yayi harbin.

Jami'in ya nuna alamun samun sauki bayan an cire alburushin daga cikin sa, bayan kwanaki kadan bayan haka ya mutu.

"Abun takaici da ban haushi. Har yanzu bamu samu damar fadawa iyalensa. Irin sakayyar da muke samu a aikin mu kenan. Muna sadaukar da rayuwar mu domin kare sauran jama'a amma idan lokacin daukaka yazo sai kaji an kirkiro wani sabon hanyar dakatar da yin haka", daya daga cikin abokan aikin sa ke nuna bakin cikin muttuwar sa.

"Ga irinta nan, sajent Lanre yana daya daga cikin jami'a da suka sadaukar da rayuwar su wajen kama Evans kuma gashi har ya mutu. Har yanzu bamu san yadda zanu bayyana ma iyalensa labarin. Abun ban haushi ne." ya kara.

An samu labari cewa jagoran tawaga ta musamman da aka kafa domin bibiyan miyagun masu aikata laifi Abba Kyari yayi jimamin mutuwar Sanusi.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement