Pulse.ng logo
Go

Sadiya Kabala Jaruma zata shiga sahu na gaba, zata shiga dakin aure

Za'a daura aurenta da angonta Ahmad Isa ranar asabar 14 ga watan afrilu da misalin karfe 1:00 na rana a masalacin al-manar dake garin kaduna

  • Published:
Jaruma Sadiya Kabala play

Jaruma Sadiya Kabala

(Instagram/official_sadiya_kabala)

An kuma samu labari mai dadi daga farfajiyar dandalin fina-finan hausa ta Kannywood, jaruma Sadiya Kabala zata amaryace.

Za'a daura aurenta da angonta Ahmad Isa ranar asabar 14 ga watan afrilu da misalin karfe 1:00 na rana a masalacin al-manar dake garin kaduna.

Za'a daura auren ta da angonta Ahmad Isa a masallacin al-manar dake Kaduna ranar asabar 14 ga wata play

Za'a daura auren ta da angonta Ahmad Isa a masallacin al-manar dake Kaduna ranar asabar 14 ga wata

(Instagram/official_sadiya_kabala)

Jarumar ta wallafa hotun katin gayyata na daurin auren a shafin ta na Instagram tare da rubuta "Assalamu alaikum jama a ina gaiyatarku maza da mata zuwa wajan daurin aure na daza ai on 14th April ah masallacin almannar dake unguwan rimi kaduna ga wanda Allah yabashe ikon zuwa ngd".

Jarumar wacce ta rasa dan'uwar mahaifiyar ranar alhamis, ta sanar cewa an daga ranar taron biki zuwa mako mai zuwa.

"Innalillahi'wainna ilaihir rajiun Allah yayima yayar mamana rasuwa yau da safe dan haka za adaura aure na on 14th April ah masallacin almannar amma zamu daga taron biki sai next week insha Allah ina mai baku hakuri" ta rubuta a shafin ta.

Ta sanar da ranar daurin auren ta tare da gayyatar dinbim masoyan ta a shafin ta na Instagram play

Ta sanar da ranar daurin auren ta tare da gayyatar dinbim masoyan ta a shafin ta na Instagram

(Instagram/official_sadiya_kabala)

 

Tauraruwar kamfanin White House tana daya daga cikin yan wasa da jarumi Adam Zango ya dauki nauyin fitowar su a masana'antar Kannywood.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.