Shahararriyar jarumar Kannywood kuma daya daga cikin iyayen masanaantar Saratu Gidado wanda aka fi sani da Saratu Daso ta fitar da hotunan ita da mijinta.

Jarumar wanda ta fiye fitowa a matsayin muguwa ko mai azabtarwa a cikin fina-finai hausa ta wallafa hotunan ne a shafin ta na dandalin sada zumunta inda take nuna farin cikin ta ga rayuwar auren su.

Cikin sakon da ta fitar bayan saka hotunan jarumar ta rubuta "Ustazai ne mu fa". Hotunan dai sun birge inda masoya masu bibiyan shafin ta suka ta kwararo masu addu'a.

A cikin wani hoton da ta sake wallafawa, jarumar ta rubuta "ku cigaba da kwararo mana Addu'a".

Saratu Gidado tana daya daga cikin jarumai mata masu harkar fim duk da auren su. A wata hira da tayi kwannan baya, tace mijinta yana mara mata bisa aikin fadarkarwa da yan fim keyi kuma bata taba nadamar aikin da take yi.

A cewar ta tana tsare mutuncin aurenta kuma tana fim kamar yadda sauran mata ke tafiyar da aikin su a ma'aikata da dama da ma masu aikin sana'ar hannu na yau da kullum.

Ta kara da cewa mai gidan ta baya jin komai ganin yanayin rawan da take takawa a fim na fitowa a matsayin mugunta domin ya san cewa wasan kwaikwayo ne.