Pulse.ng logo
Go

Kannywood Tijjani ya nuna farin ciki bisa gudunmawar da masoya suka bashi dangane da gidan shi da ya kone

  • Published:
Gidan Tijjani Asase ya kone daren ranar 3 ga watan febreru na bana play

Gidan Tijjani Asase ya kone daren ranar 3 ga watan febreru na bana

(Instagram/tijjani_asase)

Fitaccen jarumin masana'antar kannywood Tijjani Asase yana mai godiya da nuna farin ciki ga yan'uwa da abokan huldar shi na masana'antar tare da masoyan shi bisa gudummawar da suka bashi kan gidan shi da ya kone.

A daren ranar 3 ga watan febreru ne gidan jarumin ya kone tare da kayayyakin dake cikin ta. Ya sanar cewa babu abun da ya tseratar face iyalen sa domin komai dake cikin gidan ya kone sakamakon gabarar.

Jaruman kannywood sun kai ma Tijjani Asase agaji sakamakon gidan shi da ya kone play

Jaruman kannywood sun kai ma Tijjani Asase agaji sakamakon gidan shi da ya kone

(Instagram/tijjani_asase)

 

Bayan sanarwar da yayi shafin sa na kafafen sada zumunta kan wannan jarabtar da ya abkar masa, jarumai sabbi da tsofaffi tare da jiga-jiga masu ruwa da tsaki a masana'antar Kannywood sun ziyarci gidan domin jajenta masa.

A post shared by tijjani (@tijjani_asase) on

 

Bayan ziyarar da addu'o'in da jarumai suka kai masa, wasu daga cikin su sun agaza masa da kayan abinci da kudi har da sutura.

"Salam barkanmu da safiya da mika godiyata ga iyayan gidana da yayyena wa'yan da suka tayani da alhini. wasu a waya wasu hargida wasa harda gudun mawa sutura da abinci wasu harda kudi nagode Allah yabar zumunci amin nagode". ya rubuta a shafin sa na instagram.

tsofafin yan fim sun ziyarci gidan jarumin don yi masa jaje play

tsofafin yan fim sun ziyarci gidan jarumin don yi masa jaje

(instagram/tijjani_asase)

 

Game da wannan abun farin ciki da yan'uwa suka yi mashi wannan jarumin ya kasa boye nuna godiya kan ranar da suka nuna mashi. A cewar sa har ma wadanda yake tunanin cewa makiyin shine sun taya shi jaje.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.