Pulse.ng logo
Go

12 ga watan Yuni Iyalen marigayi sunyi ma shugaban kasa godiya bisa karramawa da yayi

Mohammed Fawehinmi ya kara da yi gwamnati godiya bisa matakin mayar da ranar 12 na watan Yuni a matsayin ranar dimokradiya a kasar.

  • Published:
This is what the Abiolas are saying about Buhari's announcement play Iyalen marigayi Gani Fawehinmi sun nuna farin cikin su bisa karramawa da shugaban kasa yayi ma mahaifin su (Punch)

Iyalen fitaccen lauya kuma mai yaki wajen kwato yancin bil adama, marigayi Gani Fawehinmi sunyi ma shugaban kasa godiya bisa karramawa da yayi ma mahaifin su.

Shugaba Muhammadu Buhari a wata sanarwa da aka fitar ranar 5 ga wata shugaba  ya sanar cewa an sauya ranar dimokradiya daga 29 ga watan Mayu zuwa 12 ga watan Yuni don karrama zaben dimokradiya da aka gudanar cikin shekarar 1993.

Duk a cikin sanarwar shugaban ya bayyana cewa za'a karrama Gani Fawehinmi da matsayin GCON bisa rawar da ya taka wajen tabbatar da tsarin dimokrdaiya da yakin neman yancin yan kasa.

A wata hira da yayi da manema labarai, babban dan dan marigayin, Mohammed Fawehinmi ya isar da godiyar sa ga shugaban bisa matsayin da ya baiwa mahaifin su.

Yana mai cewa"Muna ma gwamnatin tarayya godiya da wannan mutuntawa. Munyi farin ciki kuma mun amince da kyautar.

Mohammed Fawehinmi ya kara da yi gwamnati godiya bisa matakin mayar da ranar 12 na watan Yuni a matsayin ranar dimokradiya a kasar.

Bayan Fawehinmi, shugaban zai kuma karrama Babagana Kingibe wanda ya tsaya takara tare da Moshood Abiola a matsayin mataimakin sa. Zai samu kyautar GCON.

 

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.