Pulse.ng logo
Go

A garin Katsina Wajen yin lalata da kananan yara Inspeto ya rasa al'aura

Yan unguwar sun shaida cewa Inspeto wanda ba'a bayyana sunansa ba yayi kaurin suna wajen yin lalata da kananan yara maza.

  • Published: , Refreshed:
Little boy cuts off private part of policeman who tried to rape him play Hoton wani da aka yanka azzakarin sa (Press)

Wani Inspeto na rundunar yan sanda ya rasa azzakarin sa yayin da yake neman yin lalata da wani yaro dan shekara 13.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito lamarin ya faru ne a garin Tudun Markabu na karamar hukumar Faskari ya jihar Katsina a daren ranar talata 10 ga wata.

Yan unguwar sun shaida cewa Inspeto wanda ba'a bayyana sunansa ba yayi kaurin suna wajen yin lalata da kananan yara maza.

Labari ya nuna cewa jami'in hukumar tsaro ya gamu da bakar jaraba sakamakon tarkon da wasu fusatattun matasan garin suka saka masa.

Majiya sun shaida cewa an ruga da dan sanda babban asibitin faskari bayan da jini ya cigaba da malalowa sakamakon yanka da akayi masa.

Kakakin rundunar yan sanda na jihar, Gambo Isa ya tabbatar da faruwar haka inda yace hukumar bata goyon bayan ire-iren barnar da ya faru.

Yace asibiti ta amince a mayar da jami'in babban asibitin Katsina domin jinyar raunin da ya samu.

kakakin yace rundunar zata cigaba bincike a kan lamarin kuma idan an kama jami'in da laifin aikata laifin za'a hukunta shi kamar yadda doka ta tanada.

 

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement