ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Zaben 2019 zai fi na 2015 inganci - inji INEC

Malam Aliyu Bello wanda ke magana da yawun hukumar ya bayyana hakan ga manema labarai. Yace an dauki duk wani mataki da ya kamata a bi wajen gudanar da ingantacciyar zabe.

Hukumar wanda ke shirye-shiryen zaben wanda za'a gudanar a cikin watan febreru na shekarar tace al'ummar kasar su kwantar da hankulansu game da zaben.

Malam Aliyu Bello wanda ke magana da yawun hukumar ya bayyana hakan ga manema labarai. Yace an dauki duk wani mataki da ya kamata a bi wajen gudanar da ingantacciyar zabe.

Yace gabanin zaben 2019, wadanda suka samu mafi yawancin kuri'u zasu yi nasara domin zabe ne wanda yawan jama'a zai yi tasiri ga masu takara ba akasin haka ba.

Ya kara da cewa tanadin da hukumar take yi domin tunkarar zaben shine tabbatar da ingantacciyar zabe. Mallam Aliyu yana mai cewa cikin matakin da hukumar ta dauka na tabbatar da hakan shine na raba katin rejista ga wadanda basu dashi ko wadanda suke da na wucin gadi.

ADVERTISEMENT

Hukumar dai ta karyata zargin da wasu yan kasar keyi na cewa hukumar na shirin kirkirar rumfunan zabe har 30,000 da nufin yin magudi.

Mai magana da yawun hukumar zaben ya ce, hukumar ba ta yin abu a boye, idan har hukumar zata yi wani abu, to ta kan fitar da dalilai da bayanai, sannan kuma ta bi matakai na abinda doka ta aminta da suyi.

Jadawalin zaben 2019

Tuni INEC ta fitar da jadawalin zaben shugaban kasa da sauran kujerun siyasa na kasar.

Kamar yadda shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ya sanar a cikin watan Janairu, za'a gudanar da zaben a cikin watan Febreru da Maris na 2019.

ADVERTISEMENT

Shugaban yace za'a gudanar da zaben gwamnoni a ranar 2 ga watan Maris 2019 a sauran jihohin kasa banda jihar Anambra, Bayelsa, Kogi, Edo, Ondo, Ekiti da Osun.

Bisa bayanin jagoran hukumar za'a gudanar da zaben shugaban kasa da ta yan majalisar tarayya rana guda. Haka kuma, zaben yan majalisar jiha zata wakana rana guda da ta zaben gwamnoni a 2 ga watan maris na 2019.

Hukumar dai ta fitar da ranakun fara yakin neman zaben ga masu takara.

Jam'iyu da masu takarar shugaban kasa da majalisar tarayya zasu fara yakin neman zaben tun daga ranar 18 ga watan Nuwamba na 2018 har zuwa ranar 14 na watan Febreru na 2019.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT